4 Maris 2019 - 16:40
Kasar Iran Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Zaman Lafiyar Kasashen Turai

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi ya bayyana cewa zaman lafiyan da kasashen turai suka samu a halin yanzu donn kokarin da kasar Iran ta yi ne a fagen yaki da ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bahram Qasimi yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa yaki da yan ta'adda wanda gwamnatin kasar Iran da sauran kawayen kasar Siriya suka yi a kasashen Iraqi da Siriya ne ya dawo da zaman lafiya a wadannan kasashe, amma yaki don ganin bayan wadan nan kungiyoyi kwatakwata yana bukatar hadin kai daga kasashen duniya gaba daya. 

Qasimi ya kara da cewa, zaman lafiya da aka sami a birnin Paris na kasar Farana da wasu manya-manyan biranen kasashen Turai ya samu ne don kokarin yakar kungiyoyin yan ta'adda wanda kasar Iran da sauran kawayen gwmnatin kasar Siriya suka yi a nan yankin gabas ta tsakiya. 

Daga karshe Qasimi ya kammala da cewa dole ne kasashen Turai su fahinci cewa halayensu ne ya samanda kungiyoyin yan ta'adda a duniya, tunda har yanzun da muke magana kasashen turai suna bawa wasu kungiyoyin yan ta'addar mafaka.